Birbishin Rikici

Exploring the deep-seated roots of conflict in Northern Nigeria in Hausa.

Episodes (130 available)

  • Birbishin Rikici

    Yadda Uwa Ta Yi Jiran Labarin Garkuwa Da Yayanta

    Lokacin Ramadan ne, kuma Bintu Suleiman, wata uwa kuma ‘yar kasuwa mai shekaru 55 daga Ngoshe a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, tana shirin buɗe baki tare da iyalanta.

    6 Jun 20268 mins
  • Birbishin Rikici

    Bauta A Matsayin Ungozama

    Adisu Abba wata mata ce mai shekaru 45 kuma uwa ga ‘ya’ya biyar. Ta fito daga Dikwa, Jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Tun kafin rikici ya tarwatsa rayuwarta, ta riga ta fara koyon aikin da zai zama ginshiƙin rawarta a cikin al’ummarta—ta koyi yadda ake taimaka wa mata wajen haihuwa.

    9 May 20266 mins
  • Birbishin Rikici

    Sabuwar Rayuwa Bayan Yaki

    Christie Garba mace ce mai shekaru 38, uwa ga yara bakwai, wadda ke zaune a Billiri, Jihar Gombe, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Ta kasance tana zaune a Jihar Yobe tare da iyalinta kafin rikicin Boko Haram ya addabi yankin. A wancan lokacin, hare-hare sun riga sun faru a wasu wurare kusa da su, amma ba su kai ga al’ummarsu kai tsaye ba.

    6 May 20268 mins
  • Birbishin Rikici

    Ta Rasa Komai Dalilin Boko Haram

    Gina Bashir manomiya ce mai shekaru 46 daga Askira Uba a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya. A lokacin da rikicin Boko Haram ya kai kololuwa, tana zaune a Benisheik, wani karamin gari a Borno, tare da mijinta da ‘ya’yanta shida.

    8 Mar 20267 mins
  • Birbishin Rikici

    Gudun Tsira

    Kina dauke da ciki na watanni tara, ba takalmi a ƙafa, kina gudu cikin ƙaya, kura da tsoro.

    7 Feb 20267 mins
  • Birbishin Rikici

    Hatsarin Noma A Inda Babu Tsaro

    Da can kana shafe tsawon kwanaki a gona, kana shuka iri-iri na amfanin gona kana dawowa gida da girbi mai yawa. Yanzu kuma, sa’o’i kaɗan kacal kake aiki, a ƙarƙashin sa ido na sojoji. Ba za ka iya yin nesa da gari ba, kuma ba za ka ƙara shuka amfanin gona masu tsawo ba domin suna iya ɓoye ’yan ta’adda.

    3 Jan 20267 mins
  • Birbishin Rikici

    Lokacin Da Mai Taimakonta Ya Bace

    Ka gudu don ceton rayuwarka lokacin da Boko Haram suka kai hari a garinku a Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya. Da ka dawo, sai ka tarar da makwabci ya fara gina gida a kan filin ka.

    6 Dec 20257 mins
  • Birbishin Rikici

    Neman Yanci Da Kudin Fansa

    kuna gida kuna shirye-shiryen dare, bayan sallar isha'i. Rayuwarku na cike da kalu-bale, amma aƙalla kuna tare da iyalan ku. kwatsam, ba tare da gargadi ba, mahara dauke da makamai suka mamaye kauyen ku.

    1 Nov 20257 mins
  • Birbishin Rikici

    Kwana Na Karshe A Gida

    kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana.

    4 Oct 20256 mins
  • Birbishin Rikici

    Kwana Na Karshe A Gida

    kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana.

    4 Oct 20256 mins